Gwamnatin Jihar Kano ta kara Litinin cikin Ranakun fita
1 min readGwamnatin Kano ta kara Ranar Litinin cikin Ranakun data amince al’ummar kano su fita domin siyayya.
A yanzu dai al’ummar Kano Zasu fita a Ranakun Litinin da Laraba Juma’a da kuma Ranar Lahadi.
Gwamnan ya kuma bukaci al’umma da ‘yan kasuwa dasu tabbatar da bada tazara da kuma sanya safar hanci da baki domin kaucewa daga yaduwar annobar covid 19.
Cikin Wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Abba Anwar ya san yawa hannu ta ce wajibine yan kasuwa su gudanar da harkokin kasuwancin su cikin tsari.