March 29, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ina kudaden da Buhari ya karbo

1 min read

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a nan Nigeria ta buƙaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da ƴan Najeriya sunayen mutanen da suka sace naira biliyan 800 da ya ce gwamnatinsa ta ƙwato.

Ƙungiyar ta ce ta aika wa shugaban wasika ne ta neman bayanai game da sanin waɗanda suka sace ƙuɗaden da kuma abin da gwamnatinsa ta yi da kuɗin da kuma lokacin da aka ƙwato kuɗaɗen.

Ta kuma buƙaci shugaban ya ba hukumomin yaki da cin hanci da rashawa umurnin ƙaddamar da bincike kan zargin da ta yi cewa an raba wa wasu mutane kimanin naira biliyan 51 daga cikin kuɗaden da da gwamnati ta ce ta ƙwato.

Zuwa yanzu babu wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasa game da buƙatar da ƙungiyar ta ce ta aika wa shugaban ƙasa.

Ba zan fasa ɗaure duk wanda aka kama da cin hanci ba – Buhari
Ana ce-ce-ku-ce kan yawan bashin da Buhari ke karɓa
A sanarwar da ta wallafa a shafinta, ƙungiyar ta ce, “shugaban ƙasa ne da kansa a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya ya bayya…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *