April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce Mutane 42 suka kamu da covid 19 a jiya Asabar

1 min read

Ma’ikatar lafiya ta Kano a Najeriya ta ce an sake samun mutum 42 da suka harbu da cutar korona a rana guda a cikin jihar.

Jadawalin alkaluman da ma’aikatar ta fitar ya ce akwai mutum 22 da suka warke sarai, amma babu wanda ya mutu a cikin wannan yinin, wanda hakan ke nufin adadin mamata a jimlace na nan a 50.

Alkaluman daren Asabar sun kuma nuna cewa yanzu mutum 442 ke kwance a cibiyoyin killace masu dauke da wannan cuta.

Jihar Kano na cikin jihohin da suka fi fama da annobar a arewacin Kasar yawan masu cutar da wannan sabon adadi yanzu ya kai 1,091.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *