June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

MC Tagwaye ya auri ‘yar mai bai wa Buhari shawara Maryam Uwais

1 min read
Tagwaye

Fitaccen mai barkwancin nan wanda yake kwaiwayon maganganun Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, Obinna ‘MC Tagwaye’ Simon, ya auri ‘yar Maryam Uwais, mai bai wa shugaban kasar shawara kan shirin kyautata rayuwar jama’a.

MC Tagwaye, wanda dan kabilar Ibo ne, ya auri Hauwa ranar Asabar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Karshen Instagram wallafa daga mc_tagwaye

“Ga mutanen da suke tambaya…. mun yi aure cikin farin ciki yau… godiya,” in ji Obinna ‘MC Tagwaye’ Simon.

Ita ma Maryam Uwais, ta tabbatar da auren a shafinta ta Instagram inda ta wallafa hotunan daurin auren.

“Ɗiyata, Hauwa, ta yi aure yau. Kuma na samu sabon ɗa, MC Tagwaye,” in ji ta.

Ta yi kira ga abokan arziki da sauran al’umma su yi wa sabbin ma’auratan addu’ar zaman lafiya da kariya daga Ubangiji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *