June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Saudiyya na duba yuhuwar gudanar aikin hajjin bana.

1 min read
.

Ministan harakokin addini na Saudiyya Sahibzada Noor-ul-Haq Qadri ya ce a ranar Litinin 15 ga watan Yuni, gwamnatin ƙasar za ta yanke shawara ta ƙarshe game da makomar Hajjin 2020.

Da yake bayani a wani taron tuntuɓa a ranar Alhamis, ministan ya ce gwamnatin Saudiyya za ta ɗauki matakin da ya fi dacewa saboda maniyyata aikin Hajji, sannan gwamnatin ta daɗe tana nazari tare da duba hanyoyi da dama game da aikin Hajjin.

Ya ce ana ci gaba da maharawa game da yadda za a tafiyar da aikin Hajjin a ma’aikatarsa, yana mai cewa Hajjin ba za ta kasance kamar yadda aka saba ba domin za a rungumi matakai na kaucewa yaɗuwar cutar korona.

Ma’aikatar lamurran addinin ta Saudiyya ta kuma ce ta bayar da umurni bincike kan ƙiyasin kuɗaɗen aikin hajji, idan har Saudiyya ta yanke shawarar taƙaita yawan maniyyatan da za su yi aikin Ibadar da kuma adadin kwanakin da mahajjaci zai yi.

A kwanakin baya ne dai aka buɗe Masallacin Madina bayan shafe sama da watanni biyu a rufe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *