June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan Boko Haram sun kashe mutum 90 a Borno, ‘Yan bindiga sun hallaka sama da 100 a Katsina

1 min read

..

A makon da ya gabata ne aka samu rahotanni daga jihohi biyu na arewacin Najeriya kan cewa an kashe farar hula kusan 200 a hare-haren da aka ƙaddamar kan al’ummomi a jihohin Borno da Katsina.

A arewa maso gabashin kasar, waɗanda lamarin ya faru kan idanunsu sun ce mayakan ‘yan kungiyar ISWAP – wani tsagi na Boko Haram sun kutsa kauyen Gubio inda suka buɗe wa jama’a wuta har suka kashe mutum 69, sai dai a wata sanarwa da IS din ta fitar, ta yi iƙirarin kashe mutum 90.

A yankin arewa maso yammacin ƙasar, mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa an kashe mutum fiye da 50 a hare-haren ‘yan bindiga a ƙauyen Ƙadisau da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina, sa’annan daga baya aka kai hari a garuruwan ‘Yan kara da Faskari da ‘Yan Tumaki da Dan Ali inda aka kashe sama da mutum 50.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *