Yan sanda sun sake kashe wani bakar fatan Amurka a Atlanta
1 min readShugabar ‘yan sandan birnin Atlanta ta ajiye aikinsa bayan da wasu ‘yan sanda suka harbe wani bakar fata har lahira
Erika Shields ta ajiye mukaminta ne bayan da hotunan bidiyo da masu wucewa suka nada, inda suka nuna yadda rikici ya kaure tsakanin ‘yan sandan da wani bakar fata da yake zaune cikin motarsa a wani gidan sayar da abinci.
Masu zanga-zanga sun cika titunan birnin jim kadan bayan da labarai suka fito game da kisan.
‘Yan sandan birnin Atlanta sun ce mutumin mai suna Rayshard Brooks mai shekara 27 na barci ne a cikin motarsa yayin da yake jira a kan layin sayar da abincin tafi da gidanka.