June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Daya daga cikin jami’an Jami’ar Yusuf Maitama Sule Yayi Murabus.

1 min read

Shugaban majalisar gudanarwa ta jami’ar Yusuf Maitama Sule dake nan Kano Malam Sule Yahaya Hamma ya sanar da yin murabus daga mukamin sa.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Malam Suleh Yahaya Hamma da ya aikewa sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji yace ya ajiye mukamin nasa ne bisa dalilai na kashin kai.

Cikin sanarwar Alhaji Suleh Hamma yayi godiya ga gwamnati bisa goyon bayan da ya samu a yayin gudanar da aikin sa, tare da yin fatan alkhairi ga jami’ar.

Malam Suleh Yahaya Hamma shi ne shugaban majalisar gudanarwa na farko a jami’ar Yusuf Maitama Sule da aka nada a watan Mayu na shekara ta 2013.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *