Elrufa’i ya janye jami’an tsaro.
1 min read
Gwamnatin Kaduna ta bayar da umurnin janye dukkanin shingayen da aka datse kofofin shiga jihar tare da ba jami’an tsaro umurnin su janye.
Sanarwar da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnatin jihar ta ce za a toshe hanyoyin ne kawai lokacin da dokar hana fitar dare ta fara aiki daga karshe 8 na dare zuwa 5 na safe.
Sannan gwamnati ba za ta sake tura jami’ai ba a kan iyakokin jihar.