June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a nan Najeriya.

1 min read

Daya daga cikin manyan kungiyoyin kwadago na likitoci a Najeriya ta ce ta soma yajin aiki ranar Litinin saboda rashin isasshen albashi da kuma kayan kariya musamman ga likitocin da ke yaki da cutar korona.

Gamayyar Kungiyoyin Likitoci masu neman kwarewa ta ce za ta daina aiki daga Litinin ciki har da na gaggawa da kula da masu cutar korona.

Shugaban kungiyar, Aliyu Sokomba, ya ce gwamnati ta gaza cika sharudan da aka gindaya mata, wadanda suka hada da kira da ta kara albashi ga likitocin da ke cikin kasadar kamuwa da cutar korona.

Mutum fiye da 15,000 suka kamu da Covid-19 yayin da mutum 400 suka mutu, a cewar hukumar yaki da cutuak masu yaduwa ta kasar, NCDC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *