Wata kungiya ta kalubalanci matakin gwamnatin Kano na bude gidajen Kallo.
1 min read
Kungiyar Bakin Bulo Network for Better Tomorrow ta kulubalanci matakin Gwamnatin Kano na bude Gidajen Kallon kwallon kafa tare da ci gaba da garkame Makarantu addini dana boko.
Shugaban kungiyar kwamared Muhammad Sa’id Abdullahi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a daren jiya.
Sanarwar ta kuma ce Gidajen Kallon kwallon kafa sun fi makarantun hada cinkoso amma Gwamnatin ta bawa Gidajen Kallon dama.
Sanarwar ta kuma bukaci gwamnatin data yi kokarin bude Makarantun domin samun yara masu kwazo.