‘Yan Kasuwa sun tafka Babbar asara a sakamakon annobar Covid 19.
1 min read
Kimanin makonni biyu bayan
shugaba Buhari ya soke dokar kulle a wasu manyan
biranen kasar, gwamnonin Kano da Kaduna na ci gaba
da aiki ta wannan dokar, a wani mataki na ci gaba da
yaki da cutar corona.
Koda yake gwamnonin sun sassauta dokar domin baiwa
jama’a musamman ‘yan kasuwa damar hada hada a
wasu ranaku da aka kebe, amma ‘yan kasuwa a Kano
na neman Kari, kamar yadda shugaban ‘yan kasuwar
Kantin kwari Ahaji hassan Buba ya shai dawa wakilin jaridar Bustan irin halin da suka shiga
Baya ga karancin ranakun hada hada, karayar jari
saboda illar covid 19 shine babban al’amarin da ke ciwa
‘yan kasuwar tuwo a kwarya don haka suka nemi
agajin shugaba Buhari.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da masana
tattalin arziki ke jan hankalin hukumomin Najeriya su
habbaka lamuran kasuwanin su na cikin gida a
matsayin matakin.