Biyo bayan bude gidajen Kallo da gwamnatin Kano tayi Malaman Makarantun Islamiyya sun magantu
1 min read
.
A Ranar juma’ar data gabata ne Gwamnatin jihar Kano ta sahalewa masu Gidajen kallo su cigaba da gudanar da harkokinsu wanda hakan ne ya sanya Malaman islamiyya magantuwa inda suke kalubalantar matakin.
A zantawar da jaridar Bustan daily tayi da wasu Malaman islamiyya a nan Kano sun bayyana rashin jin dadin su da matakin inda suka ce gidajen kallo na tara bata gari tare da hada cunkoso Wanda hakan ka iya haifar da yaduwar annobar Covid 19.
Haka zalika Malaman sun ce islamiyya ce gurin da ake karantar da yara ilimin addini Wanda shi ne ilimi mafi amfani ga dukkan matasa.
Sun kuma bukaci gwamnatin Kano data duba yuhuwar bude Makarantun kasancewar All…yana gaggawar amsa addu’ar yara.
Amir Abubakar da wasu dalibai sun bayyanawa Jaridar Bustan matsayin da suka shiga a sakamakon rufe Makarantu inda suka bukaci gwamnati da ta bude Makarantun kamar yadda ta sahalewa
gidajen kwallon kafa.
BNm