June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jarimar film din Hausa Kwana Casa’in ta ce babban burinta ta zama hamshakiyyar ‘yar kasuwar.

2 min read

Tauraruwar fina-finan Hausa Surayya Aminu wacce aka fi sani da
Rayya a cikin shirin talabijin na Kwana Casa’in na tashar Arewa24 ta
ce tana da burin zama hamshakiyar ‘yar kasuwa.
Fitacciyar ‘yar wasan Hausan ta bayyana hakan ne lokacin da muka yi
wata hirar musamman da ita a shafinmu na Instagram.
Kodayake ‘yar wasan ta ce an haife ta ne a jihar Legas kimanin shekara
21 da suka wuce, amma ta taso ne a jihar Kaduna.
Surayya ta ce ta shahara ne sanadiyyar fitowarta a wasan Kwana
Casa’in, amma ta fara wasan Hausa ne wata shida kafin nan.
“Na yi fina-finai kamar Hanyar Arziki da Yarena da Kanin Miji da wasu
da ba su fito ba tukunna,” in ji ta.
Har ila yau ta ce tun tana karama take sha’awar aikin jarida wanda
yana daya daga cikin abubuwan da suka sa ta fara sha’awar shiga
harkar fim.
Waƙar da na yi wa Jonathan ta jefa ni cikin ruɗani – Asnanic
Yadda bidiyon rawar matan aure ya tada ƙura a Nigeria
‘Abin da ya sa na daina sumbatar mata a fina-finan Nollywood’
Ali Nuhu ne jarumin da ya fi burge ta, kamar yadda ta ce kuma a
bangaren mata ta fi son Rahama Sadau da Fati Muhammad.
Daga nan Surayya ta ce yanzu haka tana karatun difloma ne a bangaren
aikin jarida kuma tana da burin ci gaba da karatunta zuwa matakin
digiri har ma gaba da haka.
Amma ta ce a halin yanzu tana kasuwanci, inda take harkar samar da
lantarki daga kimiyyar rana wato Solar.
A karshe ta ce tana da burin zama hamshakiyar ‘yar kasuwa kuma a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *