July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kasar saudiya ta fitar da ka’idojin gudanar da ibada.

2 min read

Hukumar Haramain ta fitar da wannan sanarwa ne a shafinta na Twitter
a ranar Talata, sai dai ta ce sanarwar ba ta nuni da ranar da za a bude
masallacin ga masu Umara da masu Dawafi.
Ta ce an fitar da wadannan matakai ne bayan da kwamitin kwararru na
masallacin ya yi bincike kan yadda abubuwa za su kasance a lokacin
da aka bude masallacin don yin Umara da Dawafi.
Matakan sun hada da:

 1. Za a dinga amfani da Kofar Sarki Fahad don shiga harabar Dakin
  Ka’aba don a samu sarari sosai da kuma Kofar Jisr Annabi da Kofar
  Safa don masu ibada su samu damar fita daga harabar Ka’aba ta
  hanyar bin matakalar bene.
 2. Za a ware kofofi masu lamba daga 89 zuwa 94 don shiga harabar da
  ake Dawafi ta kasa da kuma fita ta Kofar Ajyad
 3. Za a dinga amfani da Gadar Ajyad da ke kudancin masallacin da
  Gadar Shabeika da ke yamma don shiga harbar da ake dawafi ta kasa.
  Su kuwa matakalar bene masu amfani da inji da Gadar Safa za su zama
  wajen fita
  Harin Masallacin Ka’aba na 1979 da ya sauya tarihin Saudiyya
  Hajj 2019: Amsar tambayoyinku kan ayyukan da suka shafi Hajji
  Coronavirus: Shekarun da ba a yi Aikin Hajji ba a tarihi
 4. Za a samar da hanyoyi da dama da mutane za su dinga bi don shiga
  harabar Ka’aba don tabbatar da cewa an bi dokokin yin nesa-nesa da
  juna tsakanin masu ibada
 5. Za a dinga amfani da sabon bangaren Sarki Fahad da Sarki Abdullah
  don samun isasshen waje ga masu sallah
 6. Za a dinga dawafi a harabar dakin ka’aba da kasa, amma za a bar
  hawa na farko ga tsofaffi da marasa karfi don yin dawafi
 7. Za a sanya shinge uku a wajen yin dawafi don raba tsakanin masu
  dawafi a kokarin bin dokar yin nesa-nesa da juna
 8. Za a rufe duk wata hanya ta shiga garin Makkah da sassafe
  musamman a ranar Juma’a
 9. Za a bukaci otel-otel da ke kusa da Harami su dinga kayyade yawan
  bakinsu da za su shiga cikin masallacin sallah, za a so su dinga
  shawartar bakin da su dinga bin sallar daga masaukinsu
 10. Za a kirkiri wata manhaja mai suna Tawakkalna da za a dora a
  wayoyin komai da ruwanka wacce mutane za su dinga neman izinin
  shiga masallacin a kanta
 11. Za a sanya shingayen bincike a kan hanyar zuwa Harami da kuma
  harabarsa
 12. Za a hana shiga garin Makkah daga karfe 9 na safe har zuwa 8 na
  dare ga duk wadanda ba mazauna birnin ba da kuma wadanda ba su da
  izinin shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *