June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyoyin Arewacin Kasar nan sun gudanar da zanga-Zanga.

2 min read

Kungiyoyi da dama ne suka fatsama kan tituna a birnin Katsina da ke
arewacin Najeriya ranar Talata da safe inda suka yi kira a dauki mataki
game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.
Masu zanga-zangar, mai taken #ArewaIsBleeding a turance, wato ‘Jini
yana kwarara a Arewa’, sun bayyana matukar bacin ransu kan halin ko-
in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-
kashe a yankin.
Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke
arewacin kasar don matsa lamba ga gwamnati ta dauki matakin da ya
dace kan masu kashe-kashen.
Rahotanni sun nuna cewa makon da ya gabata kadai ‘yan bindiga da
mayakan Boko Haram sun kashe mutum fiye da 100 a hare-haren da
suka kai jihohin Katsina da Borno.
Kusan mutum 200 aka kashe a Katsina da Borno a makon da ya
gabata

NorthernLivesMatter: Ƴan Nigeria sun dawo daga rakiyar

Shugaba Buhari ne?
Taɓarɓarewar tsaro: Shin Buhari ya yi watsi da jihar Katsina ne?
Gwamnatin kasar ta sha cewa jami’an tsaro suna magance matsalar
tana mai cewa galibin hare-haren da ake kai wa na gyauron ‘yan
bindiga ne, ko da yake ‘yan kasar na cewa hakan ba gaskiya ba ne.
Ranar Litinin kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International
ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan ‘yan kasara yayin da
matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin
kasar.
Wani rahoto da kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a
kasashen duniya, International Crisis Group, ta fitar a watan jiya ya ce
an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin
kasar cikin shekaru 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *