July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wani Likita ya fitar da sakamakon mace -macen da aka ringa samu a nan Kano a kwanakin baya.

1 min read

Wani farfesa Kuma likita a asibitin Aminu Kano Dr Muktar Gadanya ya ce sakamakon mace macen da akayi a kwanakin baya a Kano ya nuna cewa kaso 15.9 cikin 100 na wadanda suka rasu ana kyautata zaton cutar Corona ce ta kashesu.
Dr Muktar Gadanya ya bayyana hakan ne a yau talata a yau lokacin da yake gabatar da jawabi akan musabbabin mace macen a fadar Gwamnatin Kano.
Ya kara da cewa sauran mace macen kamar yadda binciken ya nuna sun faru ne sanadiyyar firgita da mutane suka yi na rashin zuwa asibiti idan basu da lafiya don gudun kamuwa da Corona da sauransu.
Da yake jawabi Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje Jim kadan bayan kammala gabatar da rahoton musabbabin mace macen ya ce zaa mika rahoton ga shugaban kasa tare da ministan lafiya Sannan Kuma rahoton zai taimaka wajen wayar da kan mutane akan musabbabin mace macen da suka faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *