June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za’a yiwa hukumar ‘yan sanda sauyi a Amurka.

2 min read

sauye-sauye
Shugaba Trump na Amurka ya rattaba hannu kan dokar yi wa hukumar
‘yan sandan kasar wasu sauye-sauye.
Gyaran fuskar zai hada da samar da kudaden kara bayar da horo ga
‘yan sanda, da kuma samar da hanyoyin sa ido kan irin cin zarafin da
suke yi ga al’umma.
Daga yanzu kuma jami’in tsaro ba zai sake cakumo wuyan wanda ake
zargi ba idan har ba rayuwarsa ce a cikin hadari ba.
Amurka ta fuskanci karin matsin lamba kan yin garambawul ga
hukumar ‘yan sandanta tun bayan kisan bakar fatar nan George Floyd
da wani dan sanda farar fata ya yi.
17:51
Wani jagoran addinin kirista dan Amurka ya amsa laifin lalata da
kananan yara mata
Wani jagoran addinin kirista dan kasar Amurka ya amsa laifin lalata da
kananan yara mata, a wani gidan marayu da ya bude shi da mai
dakinsa a Kenya.
A shari’ar da aka masa a wata kotu da ke Amurka, Gregory Dow ya
amsa laifuka hudu na lalata da ‘yan matan a tsakanin shekarun 2013
zuwa 2014 a gundumar Bomet da ke Yammacin Kenya.
Dama Mr Dow wanda ya fito daga jahar Philadelphia ya gudu Kenya a
shekarar 2017 don kaucewa kamu, bayan da ya ji labarin cewa ‘yan
sanda na da masaniya a kan abin da ya aikata.
17:41
Wuraren shan barasa a Zambia za su ci gaba da kasancewa a rufe
Shugaban Zambia ya ce ba zai ba da umarnin sake bude wuraren shan
barasa ba da gidajen rawa duk da matsin lambar da yake fuskanta.
Yanzu Zambia ta tabbatar da mutum 1,382 da suka kamu da Covid-19,
cikin mutum 45,248 da aka yi wa gwaji. Kuma mutum 1,142 ne suka
warke, cutar kuma ta kashe 11.
Mista Lungu ya ba da umarnin rufe wuraren shan barasa ne da gidajen
rawa watanni biyu baya, sakamakon karuwar masu dauke da cutar da
ake samu.
Ya kuma karbi shawarwari daga masana game da sake bude wuraren
yana cewa har sai jami’an lafiya sun aminta da a yi hakan kafin a ba da
umarnin.
17:12
Magufuli ya yi alkawarin gudanar da zabe na gaskiya da adalci
Shugaban Tanzaniya John Magufuli ya yi alkawarin ba da damar
gudanar da zaben gaskiya da adalci a babban zaben kasar mai zuwa a
watan Oktoba, wanda ya ke neman kasar tsayawa takara a karo na biyu
Ya nemi ‘yan siyasa da su kaucewa cin mutunci da kuma tayar da fitina
yayin yakin neman zaɓe, lokacin da ya sanar da rusa majalisar dokokin
kasar kamar yadda kundin tsarin mulki ya bukata.
Magoya bayan Magufuli na masa lakabi da “Bulldozer” suna ziga shi a
matsayin shugaban da ya taimaka wajen kawo karshen matsalar cin
hanci a cikin gwamnatin kasar.
Masu sukar sa, suma na zargin sa da tauye ‘yancin fadin albarkacin
baki tun da ya karbi mulki a 2015.
Karkashin shugabancinsa, kungiyoyin kare hakkin dan adam da ‘yan
jarida sun ta fuskantar barazana, wasu saboda suna yi masa shaguɓe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *