July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Amurka ta sanya wa ‘yan Najeriya takunkumi saboda damfara.

1 min read


Hukumomin Amurka sun sanya takunkumi wa wasu ‘yan Najeriya
shida da ake zargi da aikata zamba da ta kai ta dala fiye da miliyan
shida ta intanet.
A cewar wata sanarwa ta Sakataren harkokoin wajen Amurka Mike
Pompeo, wadanda ake zargi da damfarar karkashin jagorancin wani
mai suna Richard Uzuh, sun yi sojan gona a matsayin shugabannin
kamfanoni inda aka tura masu miliyoyin daloli ba bisa ka’ida ba ta
asusun banki.
Sauran mutanen su ne Michael Olorunyomi, Alex Ogunshakin, Felix
Okpoh, Nnamdi Benson da Abiola Kayode.
Sun kuma yaudari wadanda suka fada tarkonsu, domin samun
lambobin sirri, da lakabi, da makullan asusu, da sauran bayanansu na
banki.
‘Yan damfarar sun raba dala fiye da miliyan shida a cikin tsarin na
zamba.
Wadanda suka fada tarkon soyayyar boge na ‘yan damfarar da ake
zargi kuwa, an yaudare su ne ta hanyar sakwannin imel da kuma ta
shafukan sadarwar intanit.
Sanarwar ta ce ‘yan Najeriyar sun tsere kuma ana ci gaba da nemansu
ruwa-a-jallo.
Trump zai hana masu zuwa Amurka haihuwa shiga kasar
Amurka na tuhumar ‘yan Najeriya da zamba
Sai dai kuma hukumomin Amurka sun ce an karbe ikon dukkan
kadarorinsu, da wasu abubuwan bukatunsu da ke cikin Amurka ko
wadanda ke gittawa ta cikin Amurka, kuma an haramta wa Amurkawa
hulda da su kowacce iri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *