March 29, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnan Kano yayi watsi da Rahoton mace-mace a Kano.

2 min read


Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje,
ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar kasar da ya gano cewa cutar
korona ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka
mutu a baya bayan nan.
A wata sanarwa da ya fitar, Abba Anwar, mai magana da yawun
Gwamna Ganduje, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yin
bincike kan mace-mace ya gano cewa kashi 5.9 cikin dari ne suka
mutu sanadin korona.
Gwamnan ya ambato kwamitin yana cewa: “Mutum 255 cikin 1604 da
suka mutu, wato kashi 15.9… ne suka mutu sanadin cutar korona.
Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun
magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci
saboda fargabar annobar korona.”
A makon jiya ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa
manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya
ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa
mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a
saba gani ba a jihar.
A watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya aika kwamitin na
musamman zuwa Kano don gano sanadin yawaitar mace-macen,
sannan ya sanya dokar hana fita ko da yake daga bisani Gwamna
Ganduje ya kyale mutane su ci gaba da fita a wasu ranaku.
8:23
Abin da ya sa aka dakatar da bude wuraren ibada a Lagos
Gwamnatin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriyata ta ce ta
dage lokacin da za a bude majami’u da masallatai har zuwa wani
lokaci a nan gaba.
Gwamnan jihar Babajide Olusola Sanwo-Olu ya ce an yanke hukuncin
hakan ne sakamakon yadda ake samun karuwar mutanen da ke
kamuwa da cutar korona a jihar.
A baya dai gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar bude masallatai da
majami’u a ranakun 19 da 21 na wanann wata.
A wani taron manema labarai da gwamnan ya yi ya nuna matakin
dakatar da budewar wuraren ibadun nan take na da nasaba da yadda
ake kara samun karuwar wadanda ke harbuwa da cutar coronavirus a
jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *