June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Kano ta haramta Goyan biyu a babura masu kafa biyu.

1 min read

Shugaban hukumar karota Baffa Babba Dan’Agundi ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a yammacin yau.

Baffa Babba Dan’Agundi, ya kara da cewa hukumar karota ta lura cewa wasu na neman dawo da sana’ar a caba a jihar nan a dan haka yazama wajibi a dauki wannan mataki na haramta yin goyo a babura masu kafa biyu.

Ya kuma ce hukumar karota zata fara kama duk wanda ya karya dokar yin goye a babur mai kafa biyu daga gobe alhamis sha takwas ga watan da muke ciki kuma hukumar bazata saurarawa duk wanda yakiyin biyayya ga dokar ba.

Baffa Babba Dan’Agundi ya kuma yi kira ga masu ababen hawa dasu runka sanya takunkumin rufe hanci da baki dan kaucewa kamuwa da cutar Covid-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *