Gwamnatin tarayya ta yi barazanar cewa za ta sallami dukkan jami’an lafiyar da suka kauracewa bakin aikinsu da sunan yajin aiki.
1 min read
Ministan lafiya na kasa Dr Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan a jiya Litinin yayin tattaunawarsa da tawagar da gwamnatin tarayya ta kafa tare da shugabannin kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa a birnin tarayya Abuja.
Yayin tattaunawar tasu, ministan ya yi barazanar ne yana mai cewa, duk wani likitan kasar nan da aka samu bai halarci wurin aikinsa ba a yau Laraba, to za a sallame shi.
Dr Osagie Ehanire, ya kuma umarci shugabannin asibitoci da su bude rijistar daukar bayanan ma’aikatan da ke zuwa aiki tun daga karfe 7:00 na safe zuwa 12 na ranar kowacce rana.
Haka kuma ya kara da cewa, za a dauki kwakkwaran mataki kan duk ma’aikacin da aka samu da aikata laifin.