July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hadakar Malam addini da kungiyoyi masu zaman kansu sun yi tir da kashe-kashen rayuka a Arewacin Nigeria.

1 min read

Kungiyar hadakar Malaman addini da kungiyoyi masu zaman kasu wato coalition of ulama and NGOS ta tayi kira da kakkausar murya game da kashe-kashen al’umma a Arewacin Nigeria a baya bayan nan a wasu daga cikin jahohin a arewa.

A wata sanarwa da Shugaban zauren ya fitar Farfesa Musa Muhammad Barodo ya ce duk da cewa gwamnatin Tarayya tana iya kokarinta suma jahohi suna nasu amma kullum abin Kara ta azzara yake.
Ya ce wannan rashin tsaro ya karawa al’umma fargaba da rudani a Arewacin Nigeria dama wasu daga cikin kasashe da dama.

Sanarwar ta kuma bukaci Jami’an tsaron kasar nan dasu yi dukkan mai yuhuwa wajen magance wannan matsalolin dake addabar a Arewacin Kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *