June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotun daukaka kara ta Najeriya ta tabbatar da dakatarwar da a ka yi wa shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole daga kujerarsa.

2 min read


Dama babbar kotun da ke Abuja ta dakatar da shi daga kujerar a watan Maris na wannan shekarar ta 2020, biyo bayan karar da wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka shigar, ciki har da shugaban ta na arewa maso gabas Kwamred Mustapha Salihu.
Adams Oshiomhole ya daukaka kara bayan da aka hana shi shiga ofishin helkwatar jam’iyyar da ke unguwar Wuse 2 a Abuja.
Yanzu dai an zuba ido a ga yiwuwar daukaka kara daga Adams Oshiomhole zuwa kotun koli da kuma yadda jagorancin jam’iyyar zai kasance bayan wannan hukunci.
Alkalan kotun daukaka karar a karkashin jagorancin Jostis Monica Dongban-Mensen ne su ka yanke hukuncin suna mai cewa daukaka karar dakatarwar ta Oshiomhole ba ta da ma’ana ko hujja.
Wannan sabuwar dakatarwar ta zo ne a tsakiyar dambarwar da ke faruwa a jam’iyyar APC da gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki bayan da aka hana gwamnan damar tsayawa takara.
Tuni dai jam’iyyar ta APC ta nada mataimakin shugaban jam’iyyar na kudancin Najeriya Abiola Ajimobi a matsayin mukaddashin shugabanta.
Ko da ya ke, sakataren walwalar jam’iyyar Ibrahim Masari, ya bayyana wa Muryar Amurka yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tsara nada mukaddashi a irin wannan yanayi ya kuma ce za su daukaka kara zuwa kotun koli

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *