July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Marayu da marasa galihu sittin ne suka sami tallafin abinci a nan Kano.

1 min read


Kungiyar Indabawa kurmawa Development Association dake unguwar Dan Agundi ta ce a shirye take ta cigaba da tallafawa marayu dake fadin yankin.

Shugaban kungiyar Alhaji Aminu Shareef Dikko ne ya bayyana haka yayin da kungiyar take rabon kayan abincin Wanda ministan tsaron Nigeria Bashir Salihi Magashi ya bayar ga kungiyar.
Malam Aminu Shareef ya kuma ce ba wannan ne karan farko da kungiyar take gudanar da irin wannan tallafi ba,hadda ko da azumi sun gudanar da irin wannan tallafi ga marayu.

Wasu daga mutane da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su tare da kira ga sauran al’umma da suyi koyi da irin wadannan mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *