April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rundunar ‘yan sandan Nigeria ta bayyana dalilin kama Shugaban kwamitin amuntattu na Northern Elder Group.

1 min read

Dalilin ‘yan sanda na kama shugaban waɗanda suka yi zanga-zanga a
Katsina
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya,Coalition of Northern Groups
(CNG), ta ce rundunar ‘yan sandan ƙasar ta kama Nastura Ashir Sharif,
shugaban kwamitin amintattunta saboda zargin ya zagi Femi Adesina,
mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari.
Mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin, Abdul-Azeez Suleiman, ya
shaida wa BBC ranar Laraba cewa an kama Ashir Sharif bayan sun
kammala zanga-zanga a birnin Katsina inda suka yi kira a ɗauki mataki
game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.
Ya ce an tafi da shi hedikwatar rundunar da ke Abuja, babban birnin
kasar inda yake tsare yanzu haka.
Sanarwar da suka fitar tun da fari ta ce “kungiyar CNG ta yi matuƙar
kaɗuwa ganin cewa gwamnatin da ke iƙirarin kare mulkin dimokradiyya
za ta iya hantarar mutanen da suka fito don kare nauyin da ƙundin
tsarin mulki ya dora musu”.
Masu zanga-zangar, mai taken#ArewaIsBleeding a turance, wato ‘Jini
yana kwarara a Arewa’, sun bayyana matuƙar ɓacin ransu kan halin ko-
in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-
kashe a yankin.
Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke
arewacin ƙasar don matsa lamba ga gwamnati ta ɗauki matakin da ya
dace kan masu kashe-kashen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *