June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yanzu Yanzu Amurka ta bawa Buhari Umarni kan zubar da jini a Arewacin Nigeria.

1 min read

Amurka ta yi tir da kisan gillar farar hula da ake yi a
arewacin Najeriya.
A sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ta bayyana
cewa a kwanakin baya, wasu da ake zargin ‘yan kungiyar ISWAP ne sun
kai hare-hare a Borno inda suka kashe sama da farar hula 120, ciki har
da mata da ƙananan yara da tsofaffi.
Ta kuma ce a ranar 9 ga watan Yuni, wasu ɓarayi da ba a san ko su
wane ne ba sun kai hari a wani ƙauye a Katsina inda suka kashe
gwamman mutane.
Duka waɗannan hare-haren sun biyo bayan kashe wani fasto da
matarsa mai ciki a ranar 1 ga watan Yuni da kuma kashe wani limami
da kuma wani mai gari da farar hula masu dimbin yawa a ranar 5 ga
watan Yuni a wani rikicin ƙabilanci a Taraba.
Dubban farar hula ne suka rasa rayukansu a Najeriya a ‘yan shekarun
nan sakamakon hare-haren masu tayar da ƙayar baya, da kuma rikicin
ƙabilanci ko kuma na addini.
Gwamnatin Amurka na kira gwamnatin Najeriya da ta ƙara ƙaimi wajen
kawo zaman lafiya da kuma hukunta masu hannu a tayar da zaune
tsaye.
Kungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta ce
gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan ‘yan kasar a yayin da
matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *