June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Barcelona na son riƙe Messi har 2023, Ronaldo na son komawa MLS

2 min read

Cristiano Ronaldo

Barcelona ta yi wa kaftin ɗinta ɗan ƙasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 32 tayin sabuwar yarjejeniya domin ya ci gaba da murza leda a kulob din har 2023. (Mundo Deportivo via Metro)

Dan wasan gaba na Sifaniya Pedro, mai shekara 32, ya amince ya koma Romaamma zai yanke shawarar ko zai tsawaita zamansa na ɗan wani lokaci a Chelsea har zuwa ƙarshen kaka. (Guardian)

Pedro ba ya son kammala kaka tare da Chelsea domin ba ya son a samu cikas kan komawarsa Roma. (The Athletic – subscription only)

Dan wasan tsakiya dan kasar Scotland Ryan Fraser, mai shekara 26, yana son sama da fan £100,000 duk mako domin samun wakili bayan ya yi watsi da yarjejeniyar da Bournemouth ta taya masa kan ya ci gaba da taka leda har zuwa ƙarshen kaka. (The Times – subscription only)

Leicester City ba ta son sayar da ɗan wasan Ingilila mai shekara 23 Ben Chilwell idan an bude kasuwar musayar ƴan wasa ko da kuwa an taya ɗan wasan kan kan fam miliyan £50. (Sky Sports)

Bayern Munich na tunanin sayar da dan wasan Austria David Alaba, mai shekara 27. (Telegraph – subscription only)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya buƙaci shugabannin kulub din mara masa baya domin ya yi zubin sabbin ƴan wasa idan an bude kasuwar musayar ƴan wasa – bayan Chelsea ta amince ta kashe fan miliyan 54 domin karɓo ɗan wasan Jamus Timo Werner, mai shekara 24, daga RB Leipzig. (Mirror)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *