July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Bashir Tofa ya gargaɗi Buhari kan kama masu zanga-zanga a Katsina

1 min read

Fitaccen dan siyasar nan na Najeriya, wanda ya tsaya takara a zaben 1993, Alhaji Bashir Usman Tofa, ya gargadi shugaban Najeriya da ya sa a saki shugaban kungiyoyin da suka yi zanga-zanga kan tabarbarewar tsaro a Arewacin kasa kafin matasa su hasala su soma tayar da hankali.

Ranar Talata rundunar ‘yan sandan ƙasar ta kama Nastura Ashir Sharif, shugaban kwamitin amintattunta na Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Coalition of Northern Groups (CNG) bayan sun yi zanga-zanga a birnin Katsina.

Masu zanga-zangar, mai taken#ArewaIsBleeding a turance, wato ‘Jini yana kwarara a Arewa’, sun bayyana matuƙar ɓacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin.

A sakon da ya fitar ranar Laraba tsohon dan siyasar ya yi kira ga shugaba Buhari da Babban Sufeton ‘yan sanda da shugaban hukumar DSS “su yi gaggawa su sake shi [Nastura] domin idan samarin nan suka kufula suka fara barna a kasar nan, wallahi ba a san inda za ta tsaya ba.”

Alhaji Bashir Tofa ya kara da cewa “ba karamin rashin dabara ba ce, ba karamin rashin hikima ba ce” kama Nastura Ashir Sharif ganin cewa babu wanda ya tayar da hankali lokacin zanga-zangar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *