June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

China za ta soke bashin-da-ba-ruwa da take bin kasashen Afirka

1 min read

Shugaban China Xi Jinping ya sanar cewa kasarsa za ta za ta soke basukan-da-ba-ruwan da take bin kasashen Afirka, wadanda suka kamata a soma biya a karshen 2020.

Ya shaida wa mahalarta taron da ake yi ta intanet tsakanin China da Africa kan shawo kan cutar korona ranar Laraba cewa kasarsa za ta tsawaita lokutan biyan bashi mai ruwa da take bin kasashen Afirka da Covid-19 ta fi iya illa.

Ya kuma bukaci cibiyoyin da ke harkokin kudin kasar da su gudanar da “tattaunawa irin ta abokai” da kasashen Afirka domin “tsara yadda za su ba su bashin kasuwanci”.

“China za ta hada gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya, da Hukumar Lafiya ta Duniya da sauran kawayenta domin taimaka wa Afirka wajen yaki da Covid-19, kuma za mu yi hakan ne ta hanyar da Afirka take so,” in ji Shugaba XI.

A game da riga-kafin cutar korona, shugaban na China ya ce nahiyar Afirka za ta kasance daya daga cikin wadanda za su soma cin moriya idan kasarsa ta samu riga-kafin cutar. Ya ce China za ta ci gaba da gina asibitoci a Afirka.

Ya kara da cewa za su gina cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afirka a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *