Jama’atu Nasril Islam ta koka kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya.
1 min read
Kungiyar Jama’atu Nasril Islam da ke karkashin mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya ta koka kan halin rashin tsaro da ake fama da shi a wasu sassan arewacin kasar.
A wata sanrwa da kungiyar ta fitar, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta dauki kwararan matakan kawo karshen hare-haren da ake fama da su a yankin, tana mai cewa alkawuran da gwamnatin ke yi ba tare daukar wani mataki ba ba za su taba wadatarwa ba.
Dr. Khalid Aliyu shi ne babban sakataren kungiyar wanda kuma shi ne ya sa hannu kan sanarwar, daga Abuja Yusuf Ibrahim Yakasai ya nemi karin bayani daga gare shi kan abin da sanarwar ta kunsa.