July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kasar Nijar ta soke zuwa Aikin Hajjin bana 2020.

2 min read

Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta ce ta dauki matakain cewa kasar ba za ta je Aikin Hajjin bana ba saboda annobar cutar korona.

Ta dauki wannan matsaya ne bayan ta yi wata ganawa da masu ruwa da tsaki kan sha’anin Aikin Hajj da Umara don bayyana musu matsayar kasar game da tafiya hajjin na 2020 a ranar Alhamis.

Gwamnatin ta ce hakan na zuwa ne bayan da ta yi nazari kan sharuddan da hukumomin Saudiyya suka gindaya.

Gwamnatin ta kuma kira ga masu kamfanonin zirga-zirga Aikin Hajji da su daina karbar kudin mutane, su kuma biya basussukan da ke kansu don bai wa hukumar da ke da alhakin shirya Aikin Hajji da Umara damar ita ma ta biya masu kamfanonin jiragen sama da ke bin ta bashi.

Har yanzu Saudiyya ba ta bayyana matakin da ta dauka dangane da Aikin Hajjin bana ba, amma a ranar Lahadi 14 ga watan Yuni ministan harakokin addini na Saudiyya Sahibzada Noor-ul-Haq Qadri, ya ce a ranar Litinin 15 ga watan Yuni, gwamnatin ƙasar za ta yanke shawara ta ƙarshe game da makomar Hajjin 2020.

Sai dai har yanzu kasar ba ta fadi matsayar tata ba.

A ranar Talata ne hukumar da ke kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki na Makkah da Madina wato Haramain ta fitar da sabbin matakai da aka dauka don rage cunkoso idan aka dawo da yin Umara da Dawafi nan gaba, a kokarinta na rage sake yaduwar cutar korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *