Mutane 587 suka kamu da Corona Virus a Najeriya a jiya Laraba.
2 min read
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta nuna cikin alƙaluman da ta fitar daren Laraba cewa cutar korona ta sake kama mutum 155 a Legas, jihar da annobar ta fi tsanani a Najeriya.
Cutar kuma ta sake ɓulla a jihohin Sakkwato da Kebbi, inda hukumar NCDC ta ce an samu mutum ɗaya da ya kamu da cutar a jihohin.
Ƙididdigar ta kuma nuna cewa cutar korona ta ƙara kashemutum 16 cikin sa’a 24 a ƙasar. Yawan waɗanda suka mutu sanadin cutar tun bayan ɓullarta a Najeriya, 469.
Amma daga cikin wadanda aka tabbatar da sun kamu da cutar 17,735, an sallami waɗanda suka warke 5967 daga cibiyoyin killace majinyatan cutar, bayan an tabbatar da warkewarsu.
A lokaci guda kuma, an sake gano mutum 67 da korona ta shafa ranar Talata a Abuja, babban birnin ƙasar.

- Coronavirus: Taswirar da ke nuna yawan wadanda suka kamu a duniya
- Adadin masu coronavirus a kasashen Afrika
- Coronavirus: Abubuwan da ya kamata ku dinga yi
- Coronavirus a Najeriya: Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar

Ƙarin jihohin da aka samu sabbin masu korona, akwai Edo inda aka gano mutum 75. Sai Rivers 65, jihar Oyo kuma 56.
An kuma ba da rahoton cutar ta sake harbin mutum 25 a jihar Bayelsa, a Kaduna 18, haka ma Filato mutum 18.
Jihar Enugu mutum 17, sai Ogun mutum 12, haka ma a Borno, an gano sabbin waɗanda suka kamu mutum 12. Ondo kuma mutum 7.
Sai jihar Kwara mutum huɗu, yayin da kuma Kano da Gombe aka samu ƙarin mutum biyu biyu.

Muhimman bayanai kan annobar korona
An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.
A ranar Juma’a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.
Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa’i da Seyi Makinde da kuma Okezie Ikpeazu duk sun kamu da annobar amma sun warke ban da gwamnan Abia wanda ya kamu da cutar a baya-bayan nan.
Jiha ɗaya ce kawai ta rage yanzu a Najeriya, cutar ba ta ɓulla cikinta ba wato jihar Cross River.
Wasu dai na zargin cewa mai yiwuwa annobar ta shiga jihar, rashin yin gwaji ne ya sa ba a iya gano ta ba.
Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya yawan gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji fiye da dubu ɗaya cikin sa’a 24.