Rundinar ‘yan sandan Nigeria ta saki Nastura Ashir Shareef.
1 min read
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya,Coalition of Northern Groups (CNG), ta tabbatar da sakin shugaban kwamitin amintattu na ƙunigyar wato Nastura Ashir Sharif bayan ya shafe kwanaki biyu a hannun ‘yan sanda.
A sanarwar da mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin, Abdul-Azeez Suleiman ya sanya wa hannu, an saki Nastura ne sakamakon matsin lamba da ƙungiyarsu ta yi wa gwamnati tare da Ƙungiyar Dattawan Arewa da wasu kuma masu faɗa a ji na arewacin Najeriya da dai sauraren ƙungiyoyi.
A hirarsa da BBC, Abdul-Azeez Suleiman, ya shaida wa BBC a ranar Laraba cewa an kama Ashir Sharif ne bayan sun kammala zanga-zanga a birnin Katsina inda suka yi kira a ɗauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.