June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaban Kasar Amurka Trump ya nemi China ta taimake shi ya sake yin nasara a zaɓe

2 min read

Mr Trump yana so China ta sayi amfanin gona daga wurin manoman Amurka, a cewar littafin da zai fito nan gaba wanda kafofin watsa labaran Amurka suka yi sharhi a kansa.

Ya kara da cewa Mr Trump “bai san komai ba kan yadda za a tafiyar da fadar White House”.

Gwamnatin Trump tana ta kokarin ganin littafin bai fita kasuwa ba.

A tattaunawarsa da Fox News, Mr Trump ya ce Mr Bolton: “Ya karya doka. Wannan bayani ne na sirri da bai kamata ya fito fili ba kuma ba shi da izinin fitar da shi.”

“Mutum ne maras kan gado,” in ji shugaban kasar inda ya kara da cewa “na ba shi dama.”Hoton Hakkin Mallaka @realDonaldTrump@REALDONALDTRUMP

John Bolton ya zama mai bai wa shugaba kasa shawara kan sha’anin tsaro a watan Afrilun 2018 sannan ya ajiye aiki a watan Satumbar 2019. Amma Shugaba Trump ya ce korar Mr Bolton ya yi saboda ba ya bin “muradu” irin nasa.

Ya yi suna wajen tsattsauran ra’ayi game da shirin kasar kan harkokin kasashen waje kuma ya taba yin aiki a gwamnatin Shugaba George W Bush. A matsayinsa na mai bai wa shugaba kasa shawara kan sha’anin tsaro, shi ne babban mai bayar da shawara ga shugaban Amurka kan harkokin tsaro a ciki da wajen kasar.

Littafin na Mr Bolton mai shafi 577, mai suna The Room Where It Happened, zai fita kasuwa ranar 23 ga watan Yuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *