March 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An tuhumeni da laifin shirya zanga-zanga batare da izinin hukumin tsaro ba Nastura Ashir

1 min read

A wata hira ta musamman da ya yi da wakiliyar
Muryar Amurka Medina Dauda bayan an sako shi a
daren ranar Alhamis, Nastura ya ce an tuhume shi da
laifin shirya zanga-zanga ba tare da izinin hukumomin
tsaro ba, kuma an zarge shi da zagin daya daga cikin
masu magana da yawun fadar shugaban kasa Femi
Adeshina.
Nastura ya ce sun nuna wa jami’an tsaro takardar
neman izinin da suka aika wa Sufeto Janar na ‘yan
sanda Najeriya da kwamishinan ‘yan sandan jihar
Katsina mai dauke da tambarin da ya nuna an sa
hannu an kuma karbi takardar tun kafin ranar da aka
yi zanga-zangar.
“Jami’an ‘yan sanda sun kula da ni a cikin kwanaki
biyu da wuni daya da na yi a hannunsu kuma ba su
wulakanta ni ba, a cewar Sherif.
Sai dai ya kara da cewa shi bai ci abincinsu ba saboda
yanayi na tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *