June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Godwin Obaseki: Gwamnan Edo ya shiga jam’iyyar PDP.

1 min read

Gwamnan ya ce ya shiga PDP domin “na samu cimma burina na sake lashe zaben gwamnan jihar Edo.”

A makon da ya wuce ne jam’iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.

Sai dai masu lura da harkokin siyasa na ganin rikicin ubangida da yaronsa da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Adams Oshimohle kuma shugaban APC da kotu ta dakatar ne ya yi sanadin hana shi sake takara.

Ranar Talata Gwamna Obaseki ya fita daga jam’iyyar APC bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja yana mai cewa zai koma wata jam’iyyar domin neman takara a wa’adin mulki na biyu.

A makon da ya wuce ne jam’iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *