Jarimar Masana’antar KannyWood Hafsat Idris ta bukaci matasa dasu dogara da Sana’a.
1 min read
Shaharriyar jarimar Masana’antar shirya fina-finan Hausa Kanny Wood Hafsat Idris ta bukaci matasa dasu dogara da Sana’ar hannu bawai aikin gwamnati ba.Jaruma a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Hafsat Idris wadda ake wa lakabi da Hafsat Barauniya ta ce, sana’ar fim ta fi aikin gwamnati don kuwa abun da ke samu a dalilin fim ma’aikacin gwamnati ba zai taba samu ba.
Hafsat Barauniya ta bayyana cewar ta shiga fagen fim ne duba da cewar ba ta da ra’ayin zama ba tare da abun yi ba kuma da shi take gudanar da hidimomin rayuwar na yau da kullum.
Jarumar ta kuma ce ta dalilin sana’ar fim ta ko yi darusa masu yawa ta bangaran zamantakewar rayuwa haka zalika ta kara samu kwarewa a sha’anin fim din.