Marcus Rashford da wasu ‘yan Gasar Premier da wasu ‘yan wsa na kawo sauyi a Gasar.
2 min read
A ranar Talata, Marcus Rashford ya nemi a tallafa wa yara miliyan 1.3 domin samun abinci kyauta a lokacin wannan bazarar.
Tuni dan wasan na Manchester ya tara fam miliyan 20 domin kai abinci ga marasa ƙarfi a lokacin wannan annobar.
Martani mai daɗi da jama’a ke mayarwa kan irin nasarar da ɗan kwallon ya samu ya sauya tunanin jama’a da dama kan yadda ake kallon ‘yan kwallo.
Kuma Rashford mai shekaru 22, ba shi kaɗai yake amfani da sana’arsa ta taka leda ba domin taimako.
Troy Deeney
Kyaftin din Ƙungiyar Watford Troy Deeney yana cikin waɗanda suka yi fice – ba wai don kawai ya taimaka wa ƙungiyar samun ƙarin girma ba shekaru biyar da suka wuce, amma ya sauya rayuwarsa a matsayin wanda ya fi cin kwallaye
Ɗan kwallon mai shekara 31 ya taɓa shiga gidan kurkuku a 2012, a halin yanzu yana da gidauniyar tallafa wa marasa ƙarfi tare da matarsa Stacey.
An kafa ƙungiyar ne domin ta samar da kuɗaɗe ga yara masu naƙasa da ke makaranta. Ƙungiyar a halin yanzu tana tara kuɗi don gina wata cibiya ta wasanni sakamakon wata makaranta ta masu naƙasa da ke kusa da gidan dan ƙwallon a Watford.
Raheem Sterling
Sterling na ɗaya daga cikin manyan ƙadarorin da Manchester ta mallaka a cikin filin kwallo, amma ba ita kaɗai ta mallake shi ba.
A makon da ya gabata, ya fito a cikin shirin Newsnight inda aka tattauna da shi kan batun nuna wariyar launin fata a Birtaniya kuma ya kwarzanta maudu’in nan da ake ta magana a kai na Black Lives Matter, wato rayuwar baƙar fata na da amfani, zanga-zangar da ake yi a faɗin Birtaniya.
Sterling mai shekaru 25, an san shi da taimakon marasa galihu – kuma an haife shi har ya girma a Wembley, da ke Landan.
A shekarar da ta gabata, ya biya wa ɗalibai 500 waɗanda ‘yan makarantar da ya taɓa halarta ne domin su je su kalli wasan kusa da na ƙarshe tsakanin Manchester da Brighton.