June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutane 745 suka kamu da Coronavirus a jiya a Nigeria.

2 min read

Najeriya ta ba da rahoton gano sabbin masu cutar korona 745, adadi mafi yawa a rana ɗaya tun bullar cutar a ƙasar.

Yawan masu cutar yanzu ya kai 18,480, a cewar Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya.

Ƙididdigar ta kuma nuna cewa cutar korona ta ƙara kashe mutum 6 cikin sa’a 24 a ƙasar. Yawan waɗanda suka mutu sanadin cutar tun bayan ɓullarta a Najeriya, 475.

Cikin alƙaluman da hukumar ta fitar daren Alhamis ta ce cutar korona ta sake kama mutum 280 a Legas, jihar da annobar ta fi tsanani a Najeriya.

Amma daga cikin wadanda aka tabbatar da sun kamu da cutar 18,480, an sallami waɗanda suka warke 6307 daga cibiyoyin killace majinyatan cutar, bayan an tabbatar da warkewarsu.

Alƙalumman sun ce mutum ƙarin mutum 103 suka kamu da cutar a Oyo, Eboyin mutum 72 yayin da kuma aka sake gano mutum 60 da korona ta shafa ranar Alhamis a Abuja, babban birnin ƙasar.

Ƙarin jihohin da aka samu sabbin masu korona, akwai Imo inda aka gano mutum 46. Sai Delta 33, jihar Rivers kuma 25.

An kuma ba da rahoton cutar ta sake harbin mutum 23 a jihar Kaduna, a Katsina kuma 12, yayin da a Ondo kuma aka ƙara samun mutum 16.

A Jihar Kano 10 suka kamu da cutar, Bauchi kuma mutum takwas, Borno mutum bakwai, Kwara mutum biyar yayin da a Gombe cutar ta kama mutum huɗu.

Cutar ta sake kama mutum biyu a Sokoto, jihar da a baya ta bayar da rahoton cewa babu sauran mai ɗauke da cutar.

A Jihar Enugu ma an samu ƙarin mutum biyu, sai Yobe da Osun da Nasarawa da aka samu mutum ɗaya ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *