June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wani limamin Masallacin Juma’a ya bayyana matsalolin tsaro da annobar corona da yawan sabon Allah.

1 min read

Limamin Masallacin Juma’a na Izala dake Tal’udu,Imamu Usaman Adam Abubakar ya bayyana cewa matsalolin tsaro dake addabar arewacin Kasar nan tare annobar Coronavirus ka iya alakanta lamarin da yawan sabon All.. da al’umma suke yi a wannan lokaci.

Imamu Usman Adam Abubakar yayi wannan bayani ne jimkadan bayan idar da Hudubar sallar Juma’a daya gabatar a Masallacin dake Tal’udu cikin karamar hukumar Gwale a nan Kano.

Limamin ya kuma ce a’yan kwanakin nan an sami a sarar rayuka da dukiyoyin jama’a dama wanda hakan ke kara nuna cewa jawabin al’ummar musulmi su koma ga All.. domin samun dauki gareshi.

Imamu Usman Adam Abubakar ya kuma bukaci gwamnati da jami’an tsaro dasu kara dagewa wajen inganta tsaro musamman ma arewacin Kasar dama Kasa baki daya.

Matsalar tsaro a arewancin Kasar abune da ya kara daukar salo a yan kwanakin nan,inda ko a jihar Katsina sai da wasu matasa suka gudanar da zanga-zangar nuna bacin ransu da lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *