An tuhumi Ministan Lafiya a Zimbabwe da wabce kudin Covid 19
2 min read
An bayar da belin ministan lafiya na ƙasar Zimbabwe ranar Asabar bayan ya bayyana a gaban kotu bisa zargin rashawa.
An kama Obadiah Moyo ne ranar Juma’a bayan ‘yan adawa sun sako gwamnati a gaba da kuma a shafukan sada zumunta game da zargin cin hanci da rashawa kan sayo kayayyakin yaƙi da cutar korona a ƙasar.
Moyo ya fuskanci tuhuma kan rashawa da ta kai dala miliyan 20 na kwangilar da aka bai wa wani kamfanin ƙasar Hungary, wadda aka yi zargin cewa ba a bi ƙaida ba.
- Bidiyo Kalli bidiyon matar aure ‘yar dambe a Zimbabwe
- Kashi 60% na ‘yan firamare ba sa iya biyan kudin makaranta a Zimbabwe
- An tsare matar mataimakin shugaban Zimbabwe saboda rashawa
Zuwa yanzu gwamnati ba ta ce komai ba game da batun.
Moyo ne na biyu da ya fuskanci tuhumar cin hanci daga cikin ‘yan majalisar ministocin Shugaba Emmerson Mnangagwa.
Ya hallara a kotun cikin wata motar ƙasaita da gwamnati ta ba shi tare da rakiyar hadimansa, kamar yadda wakilin BBC a Harare, Shingai Nyoka ya bayyana.
Yayin shari’ar, an tuhume shi da laifuka daban-daban na karya ƙa’idojin ofishinsa sannan aka umarce shi da ya bayar da fasfonsa na tafiye-tafiye.
Ana sa ran zai sake bayyana a gaban kotun nan da ƙarshen watan Yuli.