Dan wasan Barcelona dake Kasar Spaniya Messi ka’iya cin kwallo 700
1 min read
Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Leganes da ci 2-0 a wasan mako na 29 da suka kara ranar Talata a Camp Nou.
Matashin dan wasa dan kasar Guinea-Bissau Ansu Fati shi ne ya fara cin kwallo daga baya Messi ya kara na biyu a bugun fenariri.
Kyaftin din Barcelona ya ci kwallo na 699 a Barca da tawagar Argentina a bugun fenariti, bayan da Ruben Perez ya yi masa keta a cikin da’irar Leganes.
Barcelona ta je gidan Sevilla ta kuma tashi ba ci.
Shin yaushe ne Messi zai ci kwallo na 700 kuma a wane wasan ne?