June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotu ta tuhumi ministan lafiya a Zimbabwe da karkatar da kuɗin yaƙi da cutar covid 19

1 min read

An bayar da belin ministan lafiya na ƙasar Zimbabwe ranar Asabar bayan ya bayyana a gaban kotu bisa zargin rashawa.

An kama Obadiah Moyo ne ranar Juma’a bayan ‘yan adawa sun sako gwamnati a gaba da kuma a shafukan sada zumunta game da zargin cin hanci da rashawa kan sayo kayayyakin yaƙi da cutar korona a ƙasar.

Moyo ya fuskanci tuhuma kan rashawa da ta kai dala miliyan 20 na kwangilar da aka bai wa wani kamfanin ƙasar Hungary, wadda aka yi zargin cewa ba a bi ƙaida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *