June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labarin wasanin karshen mako

2 min read

Ozil yana dab da barin Arsenal,Man utd sun yi canjas da Tot…1-1

Tsohon dan wasan tsakiya na Jamus Mesut Ozil yana son kawo ƙarshen kwangilarsa da Arsenal amma kulub ɗin yana son ɗan wasan mai shekara 31 ya ci gaba da taka leda wanda ke karɓar £350,000 duk mako saboda yanayin da aka shiga. (ESPN)

Kocin Chelsea Frank Lampard ya ƙalubalanci ɗan wasan gaba na Ingila Tammy Abraham, mai shekara 22, ya ƙara ƙwazo bayan karɓo ɗan wasa gaba na Jamus Timo Werner, mai shekara 24, daga RB Leipzig. (Metro)

Ɗan wasan gaba na Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, ya ce yana son lashe kofuna a Chelsea kuma a cewarsa zuwan Werner wani ƙwarin guiwa ya ƙara masa. (Guardian)

Ɗan wasan gaba da Ingila Andy Carroll, mai shekara 31 da kuma ɗan wasan baya na Sifaniya Javier Manquillo, mai shekara 26, suna dab da ƙulla yarjejeniya da Newcastle United. (Shields Gazzette)

Ɗan wasan tsakiya na Faransa Papa Gueye, mai shekara 21, ya amince ya koma Watford bayan kwangilar shi da Le Havre ta kawo ƙarshe amma wakilinsa ya ce ba ya son zuwa kulub ɗin bayan Arsenal ta taya shi, yayin da kuma Marseille ke cikin sahun ƙungiyoyi daga Faransa da Jamus da Portugal da ke sha’awar ɗan wasan. (Le Phoceen, in French)

Atletico Madrid ta yi watsi da tayin miliyan 150 na yuro kan dan wasanta na Portugal Joao Felix, mai shekara 20, daga wata ƙungiya a Ingila kafin ɓarkewar annobar korona. (Goal)

KocinSheffield United Chris Wilder ya ce an yi wa wasu daga cikin tawagar ƴan wasansa tayin sabuwar yarjejeniya yayin da rahotanni suka ce kulub ɗin ya tattauna da ɗn wasan baya na Ingila Chris Basham, mai shekara 31 da ɗn wasan tsakiya John Lundstram mai shekara 26, da kuma dan wasan Jamhuriyyar Ireland John Egan, mai shekara 27. (Sheffield Star)

Everton ta shiga sahun su Manchester United da Southampton da ke ribibin ɗan wasan baya na Real Valladolid Mohammed Salisu, duk da ɗan wasan mai shekara 21 ɗan asalin Ghana yana da sauran shekara ɗaya da ta rage masa kwangilar shi ta kawo ƙarshe. (Mirror)

Leeds United da ke shirin tsallakowa gasar Firimiya ta Ingila tana kuma shirin ware fam miliyan £50 domin zubin sabbin ƴan wasa idan ta tsallako gasar Firimiya. (Football Insider)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *