December 11, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Nura M Inuwa ya ce Waƙata ta taɓa mayar da aure.

2 min read

Nura M Inuwa, na ɗaya daga cikin mawaƙan zamani wanda za a iya cewa ya shahara a ƙasar Hausa, kuma ya yi wakoƙi musamman na soyayya da dama.

A wata tattaunawa da BBC ta yi da mawaƙin a Shafin Instagram da Facebook, mawaƙin ya bayyana cewa ya fara waƙa ne tun a 2007, kuma ya fara ne da waƙar siyasa.

A cewarsa, a halin yanzu waka ta zama sana’a, kuma hanya ce da zai iya isar wa mutane sako musamman idan ya ga ɓarna sai ya gyara.

Ya ce wakokinsa da dama sun kawo sauyi, domin akwai wata waƙarsa mai suna Ga Wuri Ga Waina‘ wadda a ciki ne ya yi magana kan makomar wanda ya kashe kansa.

Ya ce a sakamakon haka “akwai waɗanda suka kira ni suka ce na yi ceto, ma’ana na ƙwaci wata yarinya daga halaka, tana ƙoƙarin halaka kanta ta ji waƙar ‘Ga Wuri Ga Waina‘ ta bari”

Mawaƙin ya ce akwai waƙarsa ta Tambihi wadda a sakamakon haka ne wani mahaifi da ya yi niyyar yi wa ‘yarsa auren dole ya daina.

A irin waƙoƙi masu isar da saƙo dai da Nura ya yi akwai ta Dafin S wadda ya ce “a waƙar na yi maganganu daban-daban wanda akwai wanda ya kira ni ya ce a dalilin wannan har ya yi fushi matarsa har ta yi yaji, don haka abin da na faɗi na matsayin da so yake da shi, hakan ya ja suka yi sulhu ya dawo da abarsa.”

Nura ya bayyana cewa duk a cikin waƙoƙi ya fi son waƙar soyayya, sakamakon babu abin da ya fi so fiye da soyayya a rayuwarsa.

Ya bayyana cewa ya yi waƙoƙi da dama tun bayan da ya fara waƙa, amma waƙar da ya fi so ko kuma ta zama bakandamiyarsa ita ce Rigar Aro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *