September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Madrid da za su ziyarci Real Sociedad

1 min read

Wasab farko da suka kara a gasar La Liga ranar 23 ga watan Satumba Real ce ta yi nasara a gida da ci 3-1.

Wadanda suka ci wa Madrid kwallayen sun hada da Karim Benzema da Fede Valverde da kuma Luka Modric

Ita kuwa Sociedad ta zare kwallo daya ta hannun Willian Jose wanda shi ne ya fara cin kwallo a wasan minti biyu da take leda.

Real Madrid tana ta biyu a kan teburin La Liga, amma idan za ta ci kwallo 4-0 a wasan na Lahadi to za ta koma ta daya.

Barcelona tana ta daya da maki 65 da rarar kwallo 38, Real kuwa tana da maki 62 da rarar kwallo 35.

‘Yan wasan Real Madrid da za su fuskanci Sociedad:

Masu tsaron ragaCourtois da Areola da kuma Altube.

Masu tsaron bayaCarvajal da Militão da Ramos da Varane da Marcelo da Mendy da kuma Javi Hernández.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma James.

Masu buga gaba: Hazard da Benzema da Bale da Asensio da Brahim da Mariano da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *