April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za a bude filayen wasan kwallon kafa a Faransa ga magoya baya 5,000

1 min read

Za a fara barin magoya bayan wasanni a Faransa su rika shiga kallo daga 11 ga watan Yuli, in ji gwamnatin kasar, a kokarin da take na sassauta dokar kullen da aka kakaba saboda korona.

Amma za a bar mutum 5,000 ne kawai su rika shiga kallon da farko, kuma ana sa ran za a kara adadin daga baya.

“Za a kara fitar da wasu sabbin hanyoyin shawo kan cutar nan da tsakiyar watan Yuni tare da duba yiyuwar kara sassautawa a karo na biyu cikin Agusta,” in ji gwamnatin.

Wannan sanarwar na nufin za a ci gaba da buga wasannin French Cup da League Cup a gaban masoya kwallo – duka gasar biyu an dakatar da su ne sakamakon annobar korona.

An soke gasar French League ne a watan Afirilu, kuma yadda jerin jadawalin kungiyoyin yake haka aka tsayar da shi.

PSG da ke saman tebirin da tazarar maki 12 kan tsayar da gasar ce aka bayyana a matsayin wacce ta lashe gasar, yayin da Amiens da Toulouse aka bayyana su a matsayin wadanda suka fada rukuni na biyu na gasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *