March 29, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A yau Juma’a ne za’a fara rijistan shirin gwamnatin Nigeria na Npower.

2 min read

Ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a ta ce zata fara daukar sabbin
mutanen da za su ci gajiyar shirin nan na N-Power karo na uku a
mako mai zuwa.
A cewar ma’aikatar, matakin daukar sabbin wanda za su gajiyar
shirin na zuwa ne, biyo bayan duba yadda za a bunkasa shirin don
cin nasarar abinda ya sa aka kirkiri N-Power din tun da fari.
Haka zalika shirin na zaman bude dama ga dimbin matasan kasar
nan shiga tsarin shirin, a wani mataki na kudurin Gwamnatin
shugaba Buhari na fitar da kimanin ‘yan Najeriya milyan 100 daga
talauci.
Ma’aikatar ta ce wanda suke cin gajiyar shirin a diban farko da aka
fi sani da (Batch A) za su kammala a 30 ga watan Yunin 2020,
yayinda matasan da aka dauka a karo na biyu (Batch B) za su
karkare cin gajiyar shirin a 31 ga watan Yulin 2020.
Wannan dai na kunshe cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan
yada labaran ma’aikatar Rhoda Iliya ya fitar.
A cewar ministar ma’aikatar Sadiya Farouk ta cikin sanarwar, ta ce
Gwamnatin tarayya ta damu matuka wajen ganin ta fadada shirin da
sabbin mutanen da za a dauka, don bunkasar tattalin arziki
musamman biyo bayan annobar cutar COVID-19 da kalubalen da
aka samu a sanadiyyar ta.
Sanarwar ta kara da cewa, shirin zai baiwa mutane masu bukata ta
musamman fifiko, don su bunkasa rayuwarsu.
“Za a fara rajistar shiga shirin karo na uku daga tsakar ranar 26 ga
watan Yunin 2020.
Ma’aikatar ta cikin sanarwar ta kara da cewa, za a wallafa sunayen
mutanen da suka yi nasarar shiga shirin da zarar lokacin da aka
kayyade ya cika.
Idan ba a manta ba dai, an bullo da shirin N-Power ne a shekarar
2016 karkashin shirin tallafawa ‘yan kasa (NSIP), da nufin fitar da
dinbim al’ummar Najeriya daga kangin talauci, ta yadda za su
zauna da kafafunsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *