A Nigeria Karin samun mutume 661 sun kamu da korona.
1 min read
Ƙididdigar ta kuma nuna cewa cutar korona ta ƙara kashe mutum 19 cikin sa’a 24 a ƙasar, inda yanzu yawan waɗanda suka mutu sanadin cutar tun bayan ɓullarta a Najeriya, suka kai 506.
Cikin alƙaluman da hukumar ta fitar daren Asabar ta ce cutar korona ta sake kama mutum 230 a Legas, jihar da annobar ta fi tsanani a Najeriya.
Amma daga cikin waɗanda aka tabbatar da sun kamu da cutar 19,808 a Najeriya, an sallami waɗanda suka warke 6718 daga cibiyoyin killace majinyatan cutar, bayan an tabbatar da warkewarsu.
Alƙalumman sun ce ƙarin mutum 127 suka kamu da cutar a jihar Rivers, a Delta kuma mutum 83, yayin da kuma aka sake gano mutum 60 da korona ta shafa ranar Asabar a Abuja, babban birnin ƙasar.